logo

HAUSA

Mekdad: Takunkuman Amurka sun yi mummunan tasirin kan jama’a

2022-09-07 11:18:11 CMG HAUSA

 

Ministan harkokin wajen kasar Syria Faisal Mekdad ya bayyana cewa, takunkumai da tarnakin da Amurka ta sanyawa tattalin arzikin wasu kasashe, sun yi mummunan illa kan al'ummominsu

Mekdad ya wallafa wadannan kalamai ne a shafin Tiwita na ma'aikatar harkokin wajen Syria, a matsayin martani kan shawarar da Amurka ta yanke na baya-bayan, na tsawaita dokar nan da ta kira "Dokar yin ciniki da makiyi" da karin shekara guda, wadda ta baiwa Amurkar iznin ci gaba da kakkaba wa Cuba takunkumi. Har yanzu kasar Cuba kasa daya tilo da aka takaita a karkashin wannan doka, wadda aka aiwatar har na tsawon sama da shekaru 60 da suka gabata.

Ita ma kasar Syria wadda ke fama da rikici sakamakon yakin basasa da aka kwashe sama da shekaru 11 ana gwabzawa, tana karkashin takunkuman na Amurka, wadanda suka shafi kusan dukkanin bangarorin rayuwa a kasar ta Larabawa. (Ibrahim Yaya)