logo

HAUSA

Mamakon ruwan sama ya haddasa mutuwar mutane 103 a Nijer

2022-09-07 14:09:51 CMG HAUSA

 

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta jamhuriyar Nijer ta sanar da cewa, tun daga watan Yuni, ake sheka ruwan saman kamar da bakin kwarya a sassa da dama na kasar, inda yawan wadanda suka mutu ya kai 103.

Sanarwar ta ce, ruwan sama da aka dade ana shekawa, ya haddasa hadarukan nutsewar mutane da rushewar gidaje masu yawa, kuma ya zuwa ranar 5 ga wata, mutane 103 sun mutu, 125 kuma sun jikkata,  yayin da mutane fiye da dubu 140 suke fama da bala’in da ya haddasa matukar hasarar sana’o’in kiwo da noma. Larduna uku na Maradi, Zinder da Tawa dake kudancin kasar ne suka fi fama da wannan bala'in. (Safiyah Ma)