logo

HAUSA

Xi ya taya Brazil murnar cika shekaru 200 da samun 'yancin kai

2022-09-07 15:40:47 CMG HAUSA

 

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na kasar Brazil Jair Messias Bolsonaro, inda ya taya Brazil din murnar cika shekaru 200 da samun 'yancin kai.

Xi Jinping ya jaddada cewa, yana mai da hankali matuka kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Brazil, kuma yana son yin aiki tare da shugaba Bolsonaro, don sa kaimi ga ci gaba da zurfafa hadin gwiwar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu domin amfanin kasashen biyu da jama'arsu. (Ibrahim Yaya)