logo

HAUSA

Kasar Sin tana goyon bayan ci gaba da kasancewar kwararrun IAEA a tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia

2022-09-07 14:08:49 CMG HAUSA

 

 

Kasar Sin ta bayyana goyon bayanta, na ci gaba da kasancewar kwararrun hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA), a tashar makamashin nukiliyar Zaporizhzhia ta kasar Ukraine.

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhu na MDD game da tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia cewa, godiya ga hukumar hadin gwiwa ta Rasha da Ukraine, kan yadda babban darektan hukumar ta IAEA Rafael Mariano Grossi da takwarorinsa, suka yi nasarar kai ziyara tashar a makon da ya gabata, wadda ta taimaka wajen samun cikakkiyar fahimta, game da ayyukan cibiyoyin nukiliya da bangaren da ya lalace, ta yadda za a dauki matakan da suka dace.

Don haka, ya yi kira ga dukkan bangarori, da su dauki matakin da ya dace, don yayyafa ruwa game da halin da ake ciki, da kokarin samar da hanyar warware rikicin Ukraine cikin lumana. (Ibrahim Yaya)