logo

HAUSA

Mutanen da suka mutu sanadiyyar girgizar kasa a Luding sun karu zuwa 74

2022-09-07 14:41:30 CMG Hausa

Ya zuwa yau Laraba, adadin mutanen da suka rasu sanadiyyar girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta auku a gundumar Luding ta lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin ya karu zuwa 74, wasu 26 sun bace, kana mutane 259 suka ji rauni.

Yanzu ana nazarin yanayin da yankin ke ciki, da kuma gudanar da aikin ceton gaggawa. (Jamila)