logo

HAUSA

Sin ta taya William Ruto murnar zama sabon shugaban kasar Kenya

2022-09-06 20:28:14 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru na yau cewa, Sin na taya William Ruto murnar  zama sabon shugaban kasar Kenya, tare da fatan kasar Kenya za ta kiyaye samun zaman lafiya da kara samun bunkasuwa.

A jiya ne kotun kolin kasar Kenya ta tsai da kudurin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar da aka samu a ranar 9 ga watan Agusta, inda mataimakin shugaban kasar na yanzu William Ruto ya zama zababben shugaban kasar a hunkunce.

Game da wannan batu, Mao Ning ta bayyana cewa, kotun kolin kasar Kenya ta tsai da kudurin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar, lamarin da ya shaida cewa, an daidaita matsalar da ta shafi zaben bisa tsarin doka. Kakakin ta jaddada cewa, kasar Kenya muhimmiyar kasa ce da ta yi hadin gwiwa da Sin a gabashin nahiyar Afirka, kuma Sin tana fatan hada hannu da ita wajen sa kaimi ga raya dangantakar abota da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakaninsu. (Zainab)