logo

HAUSA

Mutane 66 sun mutu sanadiyyar girgizar kasar da ta auku a Sichuan

2022-09-06 19:52:51 CMG Hausa

 

Jimilar mutane 66 ne suka mutu sanadiyyar girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta auku jiya, a gundumar Luding ta lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin.

Hukumomin lardin sun kuma bayyana cewa, mutane 15 sun bata, yayin da 253 suka ji rauni, inda 5 daga cikinsu ke cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai, wasu 70 kuma ke cikin yanayi mai tsanani.

Lardin Sichuan ya ayyana matakin koli na aikin daukin gaggawa sanadiyyar ibtila’in. (Fa’iza Mustapha)