logo

HAUSA

Jami’in Iran: Iran na iya aiwatar da wasu matakai na daban idan kasashen yamma suka ja kafa game da yarjejeniyar nukiliyarta

2022-09-05 11:12:43 CMG HAUSA

 

Babban dan majalissar dokokin kasar Iran Mahmoud Abbaszadeh Meshkini, ya yi kira ga kasashen yammacin duniya da su kauracewa jan kafa, wajen cimma matsaya game da yarjejeniyar nukiliyar kasar da ake tattaunawa. Yana mai gargadin cewa, Iran za ta duba yiwuwar aiwatar da wasu matakai na daban, idan sassan masu ruwa da tsaki a batun suka yi jinkiri.

Meshkini, wanda mamba ne na kwamitin majalissar dokokin kasar mai lura da tsaron kasa da manufofin waje, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar IRNA cewa, Iran na maraba da yarjejeniyar cimma moriya tare, matakin da zai dace da babbar mariyar kasar.

Jami’in ya kara da cewa, kasashen yamma sun fi Iran bukatar wannan yarjejeniya, domin kuwa Iran na da wasu matakai na daban da za ta iya dauka wadanda za su amfani kasar. Kaza lika Iran ba za ta amince da duk wata yarjejeniya mai kunshe da tauye mata hakki ba.

Da yake amsa tambaya game da batun samar da kariya ga dukkanin sassa, dan majalissar ya ce aiwatar da matakan ba da kariya ga kowa, zai taimaka wajen farfado da amincewar juna tsakanin Iran da kasashen yamma.  (Saminu Alhassan)