logo

HAUSA

Rahoton Koriya ta Arewa ta zargi atisayen soja da Amurka da Koriya ta Kudu suka gudanar tare

2022-09-05 15:20:09 CMG HAUSA

 

Cibiyar binciken siyasa ta kasa da kasa ta Koriya ta Arewa, ta bayar da rahoto a ranar 4 ga wata, cewar atisayen soja da bangarorin Amurka da Koriya ta Kudu suka gudanar tare, aiki ne na nuna adawa, da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba, wanda kuma ke yunkurin jefa tsibirin Koriya cikin yanayi na yaki.

Daga ranar 22 ga watan Agusta zuwa ranar 1 ga watan Satumba, Koriya ta Kudu da Amurka sun gudanar da atisayen soja mai lakabin “Ulchi-Freedom Shield” tare a rabin karshen bana.

Kaza lika rahoton ta nuna cewa, atisayen soja da Amurka da Koriya ta Kudu suka gudanar tare, aiki ne na ta da hankali a tsibirin Koriya, da kuma ingiza fuskantar yakin nukiliya, kuma babban tarnaki ne ga tabbatar da fahimtar juna, da hadin gwiwa tsakanin al’ummun Koriya ta Arewa da ta Kudu, da kuma zaman lafiya a tsibirin Koriya. (Safiyah Ma)