logo

HAUSA

An fitar da kundin bayani mai kunshe da matakan yayata muhimmancin ilimin kimiyya a kasar Sin

2022-09-05 10:31:38 CMG HAUSA

 

Mahukuntan kasar Sin sun fitar da wani kundin bayani, mai kunshe da matakan yayata ilimin kimiyya tsakanin al’ummar kasar, matakan da ake fatan za su taimaka wajen ingiza kwazon al’umma a fannin samar da ci gaba ta hanyar yin kirkire kirkire.

Kundin wanda ofisoshin sakatariyar kwamitin tsakiya na JKS, da majalissar gudanarwar kasar Sin suka fitar tare, ya kuma karfafa muhimmancin hade matakan yayata ilimin kimiyya, da fannin kirkire kirkiren kimiyya da fasaha. Kana ya fayyace sassa daban daban na matakan da za a aiwatar domin cimma nasarar da aka sanya gaba.

An tsara cewa, ya zuwa shekarar 2025, za a kai ga fafada ayyukan yayata ilimin kimiyya tsakanin al’umma, inda masu bincike za su kara taka muhimmiyar rawa wajen yada ilimin kimiyya, ana kuma sa ran adadin al’ummar kasar ta Sin masu sani game da ilimin kimiyya zai haura kashi 15 bisa dari, kana adadin ’yan kasar masu maida hankali ga kimiyya da kirkire-kirkire zai yi matukar karuwa.

Har ila yau, kundin ya ce ya zuwa shekarar 2035, ana sa ran adadin al’ummar kasar ta Sin masu sani game da ilimin kimiyya zai kai kashi 25 bisa dari, yayin da yawaitar masu fahimtar kimiyya zai taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantaccen ci gaba. (Saminu Alhassan)