logo

HAUSA

Rasha za ta maida martani idan har kasashen EU suka kakabawa ‘yan kasar takunkumin biza

2022-09-05 10:49:53 CMG Hausa

Kakakin fadar gwamnatin Rasha Dmitry Peskov, ya ce kasar sa za ta dauki tsauraran matakan ramuwa, idan har kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turai ta EU, suka kakabawa ‘yan Rasha takunkumin takaita damar samun bizar shiga kasashen na Turai.

Dmitry Peskov, wanda ya bayyana hakan, yayin wata tattaunawa ta kafar wani gidan talabijin na Rasha, ya ce suna sanya ido kwarai kan wannan batu, za kuma su aiwatar da matakai da za su kare moriyar Rasha, ko da yake dai bai bayyana irin matakan da za su dauka din ba.

Kafin hakan, a ranar Larabar makon jiya, daya daga manyan jami’an kungiyar EU Josep Borrell, ya bayyana shawarar da ministocin wajen kasashe mambobin EU suka yanke, ta dakatar da yarjejeniyar bayar da biza ga ‘yan kasar Rasha karkashin tanajin kungiyar ta EU.

Duk da cewa ba a kai ga mayar da shawarar zuwa doka ba, idan hakan ta faru, ‘yan Rasha da dama za su rasa damar samun sabuwar bizar shiga kasashen EU a kan lokaci kuma cikin sauki. (Saminu Alhassan)