logo

HAUSA

CMG Na Kasar Sin Zai Samar Da Signar Kallon Gasar Wasannin Olympics Na Shekarar 2024

2022-09-05 21:36:23 CMG Hausa

A yau Litinin, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da kafar yada labarai ta wasannin Olympics OBS, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta samar da signar kallon gasar wasannin Olympics na shekarar 2024. Wannan na nufin CMG ta zama mai samar da signar kallon gasar wasannin Olympics da za a yi a birnin Paris a hukumance. Bisa yarjejeniyar, CMG za ta samar da signar kallon muhimman wasanni 4 da suka hada da na kwallon tebur da na raga da na hawan dutse da wasan kundunbala, yayin gasar wasannin Olympics na Paris na shekarar 2024. Haka kuma, ta zama tashar rediyo da talabijin da za ta yi mafi yawan ayyukan samar da signa ga al’umma yayin gasar.

Shugaban CMG Shen Haixiong da Yiannis Exarchos na OBS, sun halarci bikin rattaba hannun. (Fa’iza Mustapha)