logo

HAUSA

Wasu kasashen da suka daddale yarjejeniyar RCEP na fatan kara yin hada-hadar ba da hidimomi da kasar Sin

2022-09-04 16:26:03 CMG Hausa

A bana aka aiwatar da yarjejeniyar raya dangantakar abota kan hadin gwiwar tattalin arziki a dukkan fannoni ta yanki wato RCEP a hukunce. Bisa yarjejeniyar, kasar Sin ta bude sabbin hukumomin samar da hidimomi 22 ga kasashen ketare, da sa kaimi ga hukumomi 37 da su kara bude kofa ga kasashen waje, wadanda ke alamta cewa, Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje. Ban da haka kuma, kasashen da suka daddale yarjejeniyar ta RCEP da dama sun halarci bikin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na shekarar 2022 wato CIFTIS dake gudana a birnin Beijing, tare da shirya harkoki masu ruwa da tsaki.

Jami’ar kula da harkokin cinikayya ta karamin ofishin jakadancin kasar Thailand dake birnin Shanghai na kasar Sin, Jeeranun Hirunyasumlith ta bayyana cewa, sakamakon aiwatar da yarjejeniyar RCEP, ya sa aka kara shigar da kayayyaki da hidimomi zuwa kasuwar kasar Sin, kana an saukaka ayyukan kwastam, wanda ya sa kaimi ga jigilar kaya da hidimomi tsakanin Thailand da Sin.

A nasa bangare, babban wakilin ma’aikatar kula da harkokin cinikayya da masana’antu tsakanin kasa da kasa ta kasar Malaysia See Chee Kong ya bayyana cewa, an fara aiwatar da yarjejeniyar RCEP a ranar 18 ga watan Maris na bana a hukunce a kasarsa, kuma a watanni 7 na farkon bana, yawan kudin cinikayya tsakanin Malaysia da Sin ya kai dalar Amurka biliyan 114.5, wanda ya karu da kashi 20.7 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Ya ce ana sa ran za a kara samun ci gaban cinikayyar kaya da hidimomi tsakanin Malaysia da Sin a nan gaba. (Zainab)