logo

HAUSA

Gwamnatin Cuba ta soki tsawaita dokar hanata cinikayya da Amurka

2022-09-04 16:34:38 CMG Hausa

 

Gwamnatin kasar Cuba ta soki matakin kasar Amurka, na tsawaita dokar nan da take kira da hana cinikayya da abokan gaba, da shekara guda, wadda ta kare matakin Amurka na kakaba takunkumin cinikayya kan Cuba, tsawon shekaru 60.

Shugaban kasar Cuba Miguel Diaz-Canal, ya wallafa a shafin Twitter a jiya cewa, wannan laifi ya dade fiye da kima, amma juyin juya halin kasar zai iya jurewa.

Haka ma ministan harkokin wajen Cuba, Bruno Rodriguez, shi ma ya soki tsawaita dokar, wadda ta hana kulla dangantakar cinikayya tsakanin kasashen biyu.

Ya wallafa a shafin Twitter cewa, tsawaita dokar, ta sa Joe Biden ya zama shugaban Amurka na 12 da ya rattaba hannu kan tsarin dake goyon bayan manufar cin zarafin Cuba da al’ummarta, wadda kuma kusan dukkan kasashen duniya suka yi tir da ita.

Dokar wadda majalisar wakilan Amurka ta amince da ita a watan Oktoban shekarar 1917, ta ba shugaban kasa damar hana cinikayya da kasashen da yake ganin abokan gabar kasar ne, ta kuma bayar da damar kakaba takunkuman tattalin arziki. Dokar ta fara aiki kan Cuba ne karon farko a shekarar 1962, a lokacin gwamnatin shugaban Amurka John F. Kennedy. (Fa’iza Mustapha)