logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da jakadan Rasha a Sin mai barin gado

2022-09-03 17:03:06 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya jinjinawa kwazon jakadan kasar Rasha a Sin Andrey Denisov, wanda ya kammala aikin sa a kasar.

Yayin da suke ganawa a jiya Juma’a, Wang Yi ya ce Mr. Denisov, ya ba da gagarumar gudummawa wajen karfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. Ya kuma bayyana jakadan a matsayin dadadden aboki na gari ga kasar Sin, wanda ya kwashe kusan shekaru 10 yana aiki a kasar, inda ya yi matukar kokari wajen bunkasa hadin gwiwar kasashen biyu, da tabbatar da adalci a matakin kasa da kasa.

Wang ya kara da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, na ci gaba da ingiza cikakkiyar dangantakar hadin gwiwar kasashen su. Ya ce nasarorin da aka cimma, sun kuma kasance sakamako ne na kwazon da Mr. Denisov ya yi a tsawon wa’adin aikin sa.

A nasa bangare, Denisov ya ce ya shaida manyan nasarori da kasar Sin ta cimma, yana kuma hasashen kasar za ta samu karin nasarori a nan gaba. Ya ce, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, Sin da Rasha sun shiga sabon zamani na kyautata alakar su, kuma sassan biyu za su ci gaba da marawa juna baya, a dukkanin al’amura da suka shafi moriyar su. (Saminu Alhassan)