logo

HAUSA

Sassauta matakan kandagarkin cutar COVID-19 a Amurka ya haifar da mumunan tasiri

2022-09-03 17:03:57 CMG HAUSA

Tun daga watan Fabrairu na bana, jihohi daban-daban na kasar Amurka, sun sassauta matakan kandagarkin cutar COVID-19 bi da bi, jami’in rukuni mai kula da tinkarar cutar na White House ya bayyana cewa, gwamnati na yin shirin daina biyan kudin gwaji da jiyya, da allurar cutar daga lokacin kaka.

Shafin yanar gizo na jaridar “The Guardian” ta Birtaniya, ya ba da wani bayani a ran 30 ga watan Agusta cewa, tsofaffi da yara, da mutane mafiya hadarin kamuwa da ciwon, suna fuskantar mawuyacin hali saboda sassauta matakan kandagarkin da aka yi.

Ban da wannan kuma, kwalejin Brookings ta kasar Amurka, ta ba da rahoto a ran 24 ga watan Agusta, wanda ya nuna cewa, kasuwar kwadago ta Amurka na fuskantar karancin kuzari, saboda mutane da dama sun kamu da COVID-19, sun kuma bar kujerar aikinsu.

Shahararren mai jagorancin shirin Talabijin a Amurka Mehdi Hasan, ya wallafa sako a kan shafin Twitter, yana mai cewa, har zuwa yanzu, yawan mutanen da suke rasuwa saboda cutar a ko wace rana ya kai mutum 500. Wato har yanzu yawan mamata sakamakon yaduwar annobar a ko wane mako ya fi na lokacin harin “9.11”. (Amina Xu)