logo

HAUSA

Najeriya: Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 56 a jihar Jigawa

2022-09-03 17:01:42 CMG Hausa

A kalla mutane 56 ne suka rasu, yayin da sama da mutane 4,000 suka rasa matsugunansu, sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye sassa daban daban na jihar Jigawa dake arewacin Najeriya.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa a jihar Yusuf Sani Babura, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ruwan sama kamar da bakin kwarya, dake sauka tun daga watan Mayu ne ya haifar da ambaliyar ruwan, wanda ya lalata gidaje, da gonaki a sassa daban daban na kananan hukumomin jihar 27.

Sani Babura, ya ce ya zuwa yanzu, gwamnatin jihar ta kafa sansanonin tsugunar da wadanda suka rasa gidajen su guda 16. Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran masu ba da agaji, da su tallafawa wadanda wannan ibtila’i ya shafa.

A wani ci gaban kuma, ma’aikatar ayyukan jin kai da shawo kan bala’u, da ci gaban zamantakewar al’umma ta kasar, ta bukaci jimi’an hukumar ba da agajin gaggawa da su gabatar da rahoto game da halin da ake ciki, tare da gabatar da kayayyakin tallafi na gaggawa, ga al’ummun da ambaliyar ta shafa a jihar ta Jigawa, domin rage musu radadin wannan ibtila’i.

Tun a watan Mayun da ya shude ne mahukuntan Najeriya suka fitar da hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohin kasar 32 cikin 36 da babban birnin tarayyar kasar Abuja, suna masu gargadin aukuwar mummunar ambaliyar ruwa a shekarar ta bana. (Saminu Alhassan)