logo

HAUSA

Rasha za ta daina samar da man fetur ga kasashe masu goyon bayan kayyade farashinta na man fetur

2022-09-02 13:05:19 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Rasha mai kula da harkokin makamashi Alexander Novak ya bayyana cewa, kasarsa za ta dakatar da samar da man fetur da sauran hajojin man fetur nata ga kasashen da suke goyon bayan kayyade farashint man fetur na Rasha. Rasha ta ki samar da man fetur ga kasashe wadanda ba su bi ka’idojin kasuwa ba.

A ranar 31 ga watan Agusta, sakatariyar yada labarai ta fadar White House ta kasar Amurka Karina Jean Pierre ta bayyana cewa, ministocin harkokin kudin kasashen G7 za su tattauna kan batun kayyade farashin man fetur na kasar Rasha bisa shawarar shugaban kasar Amurka Joe Biden a yayin taron da za a shirya a ranar 2 ga wata. (Maryam Yang)