logo

HAUSA

MDD za ta taimakawa Ghana zurfafa rawar da mata ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya

2022-09-02 13:06:52 CMG Hausa

MDD za ta taimakawa rundunonin sojin Ghana (GAF), domin kara daukar mata da zurfafa rawar da suke takawa ga aikin wanzar da zaman lafiya.

Wata sanarwa da ofishin MDD dake Ghana ya fitar ta ce, domin gudanar da wadannan shirye-shirye, a cikin shekaru 3 masu zuwa, majalisar za ta taimakawa rundunonin da dala miliyan 3.7 daga asusun Elsie wato (EIF), wanda aka kafa domin jami’an tsaro mata dake aikin wanzar da zaman lafiya.

Da wannan tallafin na asusun EIF, ana sa ran Ghana za ta kara bayar da gudunmawar sojoji mata ta hanyar tura rundunar soji mai karfi dake da wakilcin mata daidai gwargawado, ciki har da tura mata kwamandoji ga shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake kasar Lebanon na tsawon shekaru 3 ko fiye. (Fa’iza Mustapha)