logo

HAUSA

Xi ya yi kira da a raya tattalin arziki mai salon bude kofa

2022-09-01 09:46:32 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a bude kofa ga kasashen waje, domin sa kaimi ga farfadowa da bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Xi ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar taya murna, da ya aike ga bikin baje kolin hidimomin kasuwanci na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2022 (CIFTIS), wanda aka bude ranar Laraba a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Shugaba Xi ya yi nuna cewa, CIFTIS wani muhimmin dandali ne ga kasar Sin, na fadada bude kofa ga kasashen waje, da zurfafa hadin gwiwa, da jagoranci a fannin kirkire-kirkire. Yana mai cewa, bikin CIFTIS ya ba da gudummawa mai yakini ga bunkasuwar sassan ba da hidima a duniya, gami da cinikayyar hidimomi.

Ya kara da cewa, kasar Sin ta nace kan inganta ci gaba mai inganci, da bude kofa ga ketare. Ya kuma yi nuni da cewa, kasar Sin ta sassauta hanyoyin shiga kasuwanninta a bangaren samar da hidima, da bude harkokin cinikayya tsakanin kasashe, da fadada aikin dandalin bude kofa ga waje, baya ga kokarin da take yi na kafa ingantaccen tsarin fafada sashin samar da hidima. (Ibrahim Yaya)