logo

HAUSA

An cimma nasarar gudanar da taron shawarwarin ciniki tsakanin Sin da Nijeriya

2022-09-01 13:47:11 CMG Hausa

A ranar 30 ga watan Agusta, an kira taron shawarwarin ciniki a tsakanin kasar Sin da Nijeriya ta kafar bidiyo a biranen Beijing, da Fujian na kasar Sin, da kuma wasu sassan Nijeriya. An gudanar da taron ne bisa hadin gwiwar sashen hulda da bangarorin ketare na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, da gwamnatin lardin Fujian, da ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Nijeriya da kuma gwamnatin jihar Kano. Mataimakiyar shugaban sashen hulda da bangarorin ketare na kwamitin tsakiyar JKS Shen Beili, da sakataren Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya Iyiola Omisore sun halarci taron, tare da gabatar da jawabai.

A jawabinta, Shen Beili ta ce, kasar Sin za ta karfafa mu’amalar dake tsakaninta da jam’iyyun siyasan Nijeriya, da kare dangantakar cude-ni-in-cude-ka a tsakanin kasashen duniya, da aiwatar da jadawalin raya kasa da kasa, da inganta shawarar “ziri daya da hanya daya”, da karfafa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka bisa yarjejeniyoyin da aka kulla a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC.

A nasu bangare kuma, Iyiola Omisore da wasu jami’an Nijeriya, sun yi bitar hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da Nijeriya da dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, inda suka jaddada cewa, kasar Sin aminiyar Nijeriya ce, kuma ana fatan ci gaba da habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, musamman ma a fannonin ciniki da zuba jari, da gina ababen more rayuwa, da ayyukan gona da samar da abinci da sauransu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)