logo

HAUSA

'Dimokradiyya irin ta Amurka' ta bar Iraki cikin rugujewa

2022-09-01 21:56:07 CMG Hausa

A ranar 29 ga watan Agusta, wani mummunan rikici ya barke a Bagadaza, babban birnin kasar Iraki, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 30, tare da jikkata daruruwa. Hatta yankin "Green Zone" da sojojin Amurka ke ba da kariya, an kai musu hari da rokoki. Jaridar New York Times ta ce, mai yiwuwa hakan na iya zama mafarin wani yanayi mafi hadari ga Iraki.

Tun bayan zaben da aka yi bisa tsarin "dimokiradiyya irin ta Amurka" a Iraki a shekara ta 2005, ba a taba samun nasarar kafa gwamnati ba. Bayan kusan shekaru 20 da fara aiwatar da abin da aka kira "Gyare-gyaren demokradiyya", matakin ya lalata Iraki kwarai da gaske.

A fagen siyasa, Amurka ta shigar da tsarin siyasar dimokuradiyya na yammacin duniya zuwa cikin Iraki, wanda a zahiri ya haifar da rarrabuwar kawuna a fannin siyasar kasar, kuma da wuya bangarorin siyasa daban-daban su cimma nasarar sulhu.

Ta fuskar tattalin arziki, yake-yake da tashe-tashen hankula sun haifar da asarar da ba za a iya misaltawa ba ga tattalin arzikin Iraki. Alkaluman sun nuna cewa, a shekarar 1990, GDP na kowane mutum a Iraki ya kai dala 10,356, amma ya zuwa shekarar 2020, adadin ya yi kasa zuwa dala 4,157 kacal.

A fannin tsaro, saboda rudanin siyasar da aka samu a cikin gidan a Iraki, ta'addanci ya bazu cikin sauri, kuma al'ummar kasar sun sake zama wadanda abin ya shafa kai tsaye.

Ahmed al-Sharifi, kwararre kan al'amuran da suka shafi dabarun Iraki ya yi nuni da cewa, manufar mamayar da Amurka ta yi a Iraki, ba wai don a taimaka wa Irakin wajen tabbatar da dimokuradiyya kamar yadda ta fada ba ne, sai dai don karfafa ikon Amurka a yankin gabas ta tsakiya.

A cikin shekaru 20 da suka gabata, mutane kusan miliyan daya a Gabas ta Tsakiya, sun fada karkashin rugujewar gidaje irin na "dimokradiyyar Amurka". Dole ne kasashen duniya su yi la'akari da laifukan da Amurka ta aikata a Gabas ta Tsakiya, tare da neman adalci ga wadanda suka yi hasara sakamakon hakan. (Mai fassara: Bilkisu Xin)