logo

HAUSA

Kasashen duniya da dama sun taya kasar Sin murnar kammala aikin shugabancin karba karba na kwamitin sulhun MDD

2022-09-01 11:15:29 CMG Hausa

Jiya Laraba 31 ga watan Agusta, kasar Sin ta kammala aikin shugabancin karba karba na kwamitin sulhun MDD. Kasashen duniya da dama da suka hada da kasar Brazil da hadaddiyar daular Larabawa da sauransu sun taya kasar Sin murnar kammala wannan aiki cikin watan Agusta da ya gabata, tare da yaba mata kan gudummawar da ta bayar.

A watan Agustan da ya gabata ne, kwamitin sulhu na MDD ya kira taruka sama da 20 karkashin jagorancin bangaren Sin, inda ya zartas da kudurori guda biyu, da wata sanarwar shugaba, da kuma wani rahoton zantawar shugaba.

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokarin tabbatar da zaman lafiya, da tsaro, da ci gaban kasashen duniya baki daya. A cewar jami’in Sin, tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, shi ne babban nauyin dake wuyan kwamitin sulhu na MDD, bisa la’akari da yanayin rashin tabbas da kalubaloli iri-iri, da rikice-rikice da ake fama da su a kasashe daban daban a halin yanzu, ana iya cewa, kwamitin sulhu na MDD na kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa.

Jami’in ya kara da cewa, a matsayinta na mamba a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin za ta ci gaba da sauke nauyin dake bisa wuyanta, da kuma ba da gudummawa yadda kasashen duniya suke bukata. (Maryam)