logo

HAUSA

Sin ta bukaci a warware matsalar Libya ta hanyar zaman lafiya

2022-08-31 10:36:38 CMG Hausa

Jiya Litinin, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing ya gabatar da jawabi a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun kasar Libya, inda ya yi kira ga bangarorin da batun kasar Libya ya shafa, da su kai zuciya nesa, da sa kaimin wajen warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar lumana.

Dai Bing ya ce, cikin shekaru sama da 11 da suka gabata, kasar ta sha fama da matsaloli, kuma, yanayin zaman lafiya da ake ciki a halin yanzu a kasar, ba abu mai sauki ba. Kasar Sin ta nuna damuwa game da rikici na baya-bayan nan da ya barke a birnin Tripoli, wanda ya haddasa rasuwa da jikkatar mutane sama da dari 2. Don haka, kasar Sin ta yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki, da su mai da hankali kan bukatun al’umma, su kuma kai zuciya nesa, domin warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyoyin lumana, kamar tattaunawa da tuntubar juna da kokarin kaucewa duk wani tashin hankali. Kasar Sin tana goyon bayan kwamitin hadin gwiwa na soja, domin ya ci gaba da ba da gudummawar tsagaita bude wuta da kokarin ganin sojojin haya da na kasashen ketare, sun janye daga kasar.

Ya kara da cewa, hanyar siyasa ita ce hanya daya tilo da za a bi wajen warware matsalar kasar Libya. Kuma, farfado da tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al’umma, su zama muhimman hanyoyin kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Libya. Man fetur shi ne jigon kudin shigar kasar Libya da al’ummominta. Wannan ya sa, kasar Sin take maraba da sake dawo da aikin hakar mai a kasar Libya, sannan ta bukaci dukkan bangarorin kasar, da su karfafa tuntubar juna kan yadda za a raba kudaden shigar man fetur, don tabbatar da cewa rabon albarkatun mai, ya shafi dukkan jama'a. Haka kuma, Dai ya nuna damuwa kan asarar da kwace kadarorin kasar ya haifar mata, da fatan kwamitin sulhu da kuma na sanya takunkumi, za su yi nazari yadda ya kamata tare da daukar matakin da ya dace kan bukatun kasar. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)