logo

HAUSA

Na Gaba Ya Yi Gaba….

2022-08-31 19:38:09 CMG Hausa

Da alamu dai hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, tana ci gaba da tsolewa wasu kasashe ido, wadanda a baya suke ta yunkurin kirkiro bayanai na karya da nufin bata wannan alaka mai dimbin tasiri da fa’ida ga bangarorin biyu. Amma bakin alkalami ya riga ya bushe.

Kasa ta baya-bayan nan da ta bijiro da maitarta a fili wajen ganin ta kulla alaka da kasashen Afirka, ita ce kasar Japan, inda ta shirya taron raya kasashen Afirka karo na 8 a kasar Tunusiya daga ranar 27 zuwa ta 28 ga watan Agustan shekarar 2022 da muke ciki.

A yayin taron, firaministan Japan Fumio Kishida ya sanar ta kafar bidiyo cewa, a cikin shekaru 3 masu zuwa, kasarsa za ta zuba jarin dalar biliyan 30 a kasashen Afirka, sannan za ta horas da kwararrun nahiyar dubu 300 da dai sauransu. A cewarsa wai, “Wannan aiki ya sha bamban da na kasar Sin”. Amma, idan mutum ya ce zai ba ka riga, aka ce ka kalli ta wuyansa.

Idan har Japan da sauran kasashen yamma suna son su rudi kasashen Afirka da sunan tallafi ko horas da kwararru, don kulla wata alaka ta moriyar kansu, ya kamata su san cewa, kasashen Afirka sun dade suna kuma ci gaba da amfana da hadin gwiwarsu da kasar Sin. Wannan dai wani salo ne na wayon a ci, wai an kori kare daga gindin Dinya. Amma kan Mage ya waye.

Ai ko bayan Japan da wasu kasashe, ita ma kasar Amurka ta shelanta irin wannan alkawari mai kama da romon baka, yayin taron G7 da ya gudana a kasar Jamus a wani lokaci cikin wannan shekara, inda ta yi ikirarin kafa wata gidauniya da sunan tallafawa kasashe masu tasowa, duk da neman bata sunan shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar. Koma dai mene ne, abin tambaya shi ne, me ya sa sai yanzu kasar Japan da sauran kasashen yamma ke neman kulla alaka da kasashen Afirka, bayan da Sin da Afirka suke kara cin gajiyar alakarsu mai cike da aminci da mutuntawa da kare moriyar juna a dukkan sassa? Kifi dai yana ganin ka mai jar koma. A yi dai mu gani, idan har tusa tana hura wuta. (Ibrahim Yaya)