logo

HAUSA

Sin ta gabatar da sakon ta’aziyyar tsohon shugaban tarayyar Soviet

2022-08-31 20:34:56 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta gabatar da sakon ta’aziyya ga iyalan tsohon shugaban tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev, wanda ya rasu da yammacin jiya Talata, bayan ya sha fama da jinya.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Sin Zhao Lijian, ya bayyana Gorbachev, a matsayin shugaba da ya ba da babbar gudummawa ga kyautatuwar dangantaka tsakanin Sin da tsohuwar tarayyar Soviet.  (Saminu Alhassan)