logo

HAUSA

Tauraron Dan Adam Na Farko Na Binciken Hasken Rana Na Kasar Sin Ya Samu Ci Gaba

2022-08-31 10:48:37 CMG Hausa

Hukumar kula da harkokin binciken sararin samaniya ta kasar Sin CNSA, ta bayyana cewa, tauraron dan adam na farko da kasar Sin ta harba don gudanar da aikin binciken hasken rana, ya gano fitowar hasken rana kusan 100, tare da kammala gwaje-gwajen da ya tsara yi a sararin samaniya yadda ya kamata.

Babban mai tsara aikin tauraron dan-Adam na Gaofen na kasar Sin Zhao Jian, ya bayyana a jiya a yayin taron manema labarai kan ci gaban da tauraron dan Adam din ya samu cewa, an fitar da bayanan kimiyya a hukumance tare da rabawa kasashen duniya.

Tauraron dan-Adam din mai suna Xihe, wanda aka kaddamar da shi a watan Oktoban bara, yana aiki ne a falakin rana a madaidaicin tsayin kilomita 517. (Ibrahim Yaya)