logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta dakatar da duk wata musaya da yankin Taiwan

2022-08-31 20:36:55 CMG Hausa

Kasar Sin ta bukaci tsagin Amurka, da ya dakatar da duk wani nau’in musaya da yankin Taiwan, ya kuma martaba manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyin hadin gwiwa 3 masu nasaba da hakan da sassan biyu suka amince.

Da yake tsokaci game da ziyarar da gwamnan jihar Arizona Doug Ducey ya kai yankin na Taiwan, yayin taron manema labarai na yau Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, gwamnatin Sin za ta dauki tsattsauran mataki na kare ikon mulkin kai da dunkulewar daukacin yankunanta. (Saminu Al