logo

HAUSA

Sin ta bukaci a daina keta cikakken ’yanci da yankunan kasar Syria

2022-08-30 10:17:45 CMG Hausa

Jiya Litinin, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya gabatar da jawabi a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun siyasa da jin kai na kasar Syria, inda ya bukaci a daina kasancewar sojojin kasashen ketare ba bisa doka ba, da kawo karshen ayyukan soja da suka gudanarwa a cikin kasar, da kawo karshen keta hakkin bil-Adama da cikakken ’yanci da yankunan kasar Syria.

Zhang Jun ya ce, girmama cikakken ’yanci da yankunan kasa, muhimmiyar ka’ida ce cikin kundin tsarin MDD, kuma shi ne ginshikin huldar kasa da kasa. Don haka, ya kamata a martaba dukkanin manufofin dake cikin kundin tsarin MDD yadda ya kamata. Ya kuma bayyana cewa, matakan sojan da kasar Amurka ta dauka a gabashin kasar Syria cikin ‘yan kwanakin nan, sun keta cikakken ’yanci da yankunan kasar Syria, kuma, ba su da nasaba da batun “Ikon kare kai” da aka tanada cikin kundin tsarin MDD. Dole ne a dakatar da kasancewar sojojin kasashen ketare cikin kasar Syria ba bisa doka ba, da kawo karshen matakan da suke dauka ba bisa doka ba.

Zhang Jun ya bayyana cewa, farfadowar tattalin arziki da bunkasuwa, ita ce babbar hanyar da kasar Syria za ta bi don fita daga halin da kasar ke ciki. Sai dai kuma takunkuman kashin kai na tsawon lokaci da aka kakabawa kasar, yana lalata muhimman hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasar, inda wasu kasashe suka kwashe muhimman albarkatun farfado da tattalin arzikin kasar Syria ba bisa doka ba, lamarin da ya haddasa babbar illa ga al’ummomin kasar. Don haka, a cewarsa, ya kamata a kawo karshen takunkuman da aka kakabawa kasar Syria, da kuma dakatar da kwashe albarkarun kasar ba bisa doka ba. (Maryam)