logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta mayarwa Afghanistan kadarorin ta

2022-08-30 19:49:16 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta yi kira ga gwamnatin Amurka da ta mayarwa Afghanistan kadarorin ta da ta rike a bankuna, a wannan gaba da al’ummar Afghanistan kimanin miliyan 25 ke fama da fatara.

Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta fitar, ya nuna kusan mutum 4 cikin 5 na al’ummar Afghanistan na da imanin cewa, yakin da Amurka ta yi a kasar bai tsinana komai ba, kuma daga karshe Amurka ba ta cimma manufar yakin ba.

Yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa na Talatar nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce sakamakon jin ra’ayin jama’ar, ya nuna ainihin yadda al’ummar kasar ke ji a ran su. Kuma yakin da Amurka ta yi a Afghanistan, ya ma kara fadada yawan kungiyoyin ta’addancin a kasar, tare da haifar da karin kalubale dake hana ruwa guda, a kokarin da kasar ke yi na farfadowa, har bayan shekara guda da ficewar sojojin Amurkan daga kasar.   (Saminu Alhassan)