logo

HAUSA

An bude baje kolin cinikayya mafi girma a Mozambique

2022-08-30 13:39:42 CMG Hausa

Jiya ne shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi ya bude bikin baje kolin kasa da kasa na Maputo karo na 57 da ake kira FACIM a takaice, bikin baje kolin masana'antu, da kasuwanci da hidima na kasar mafi girma, inda fiye da masu baje koli 2,000 suka halarta, ciki har da 350 daga kasashen ketare 22.

Ana sa ran baje kolin na makwanni biyu da ake gudanarwa a wajen Maputo, babban birnin kasar, zai samar da wani dandali ga kamfanoni, wadanda za su baje kolin kayayyaki da ayyukansu, da yadda ’yan kasuwa za su nemi zuba jari da ma damammaki na yin hadin gwiwa.

Da yake jawabi a yayin kaddamar da bikin, shugaba Nyusi ya bukaci masu samar da kayayyaki dake kasar, da su yi cikakken nazarin kwatankwacin fa'idodinsu, kamar yadda tattalin arzikin kasar ya nuna yanayin farfadowa bayan lafawar cutar COVID-19.

Yayin da yake jaddada muhimmancin yin la'akari da damammaki daban-daban, tare da mai da hankali kan samun damar shiga kasuwannin da suka hada da kasar Sin, da Tarayyar Turai, da kungiyar raya kasashen kudancin Afirka, shugaba Nyusi ya ce, ya kamata a gaggauta kara fadada fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, da ba da damar zuba jari a fannin aikin gona, da kamun kifi, da dabaru na hidima, da makamashin da ake iya sabuntawa, da yawon shakatawa. (Ibrahim Yaya)