logo

HAUSA

An samu ci gaba a fannin tinkarar bala’u a kasar Sin

2022-08-30 13:37:56 CMG Hausa

A yau Talata ne, aka shirya wani taron manema labaru a nan birnin Beijing na kasar Sin, don bayyana yadda ake gudanar da gyare-gyare a fannin aikin tinkarar bala’u da haduran da suka abku kwatsam a kasar. Inda Zhou Xuewen, mataimakin ministan kasar mai kula da aikin tinkarar bala’u, ya ce an kafa wani sabon tsarin da ya hada bangarorin rigakafin bala’u, da tinkararsu, da ceton jama’a, a waje guda, gami da kyautata ayyuka masu alaka da raya fasahohi, da samar da sabbin kyayyakin da ake bukata domin gudanar da aikin tinkarar bala’u daga Indallahi.

Bayanai na cewa, a shekarun baya, mutanen da suka rasu sakamakon bala’u, da yawan gidajen da suka rushe, da kudaden da aka yi asara, duk sun ragu sosai a kasar ta Sin. (Bello Wang)