logo

HAUSA

Kakakin Iran: Farfado da yarjejeniyar nukiliyar 2015 bisa moriyar dukkan bangarori

2022-08-29 09:56:17 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kanaani, ya bayyana cewa, da gaske Iran take ta cimma matsaya a Vienna, domin sake farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma a shekarar 2015, ya dace da moriyar dukkan bangarorin.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran (IRNA) ne ya ruwaito Nasser Kanaani yana bayyana hakan jiya Lahadi, inda bangarorin dake tattauna batun nukiliyar suka yi nasarar warware mafi yawan batutuwan da suka shafi farfado da yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015, wadda aka fi sani da Joint Comprehensive Plan of Action (JCPOA).

Ya ce, abin da ya faru ya zuwa yanzu a shawarwarin, na nuni da wani yanayi mai haske da kuma ci gaba, akwai kuma wasu batutuwa masu muhimmanci da suka rage wadanda ake fatan za a warware su a yayin tattaunawar.

Kanaani ya kara da cewa, Iran ta jaddada cewa, tilas ne aiwatar da duk wata yarjejeniyar nukiliyar da za a iya cimmawa, ta kasance ta ba ni gishiri in ba ka manda, kuma tilas ne dukkan kasashe su jajirce wajen cika alkawuransu.

Ya kuma yi fatan cewa, ya kamata bangaren Amurka ya yi aiki cikin hikima, da niyyar siyasa don daukar mataki bisa tsarin yarjejeniyar nukiliyar, da kuma yin la'akari da abin da Iran din take bukata. (Ibrahim Yaya)