logo

HAUSA

Shugaba Xi ya gabatar da sakon jaje ga takwaransa na Pakistan bisa matsanaciyar ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu sassan kasar

2022-08-29 21:05:55 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da sakon jaje ga takwaransa na Pakistan Arif Alvi, bisa matsanaciyar ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu sassan kasar ta Pakistan.

Tun daga watan Yuni ne ake ta tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar, lamarin da ya haifar da ambaliyar ruwa da kawo yanzu ta sabbaba rasuwar mutane 1,061, kamar dai yadda hukumar yaki da bala’u ta kasar ta bayyana, cikin alkaluman da ta fitar a jiya Lahadi. (Saminu Alhassan)