logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka ta kauracewa rura wutar rikici a zirin Taiwan

2022-08-29 21:04:26 CMG Hausa

Mahukuntan kasar Sin, sun gargadi Amurka da ta kaucewa zama mai tada husuma, da wargaza yanayin daidaito a zirin Taiwan. Wannan gargadi dai na zuwa ne kwana guda, bayan da a jiya Lahadi, wasu jiragen ruwan yaki na Amurka suka ratsa zirin na Taiwan.

Jiragen ruwan yakin biyu, Chancellorsville da Antietam, sun rasta zirin Taiwan a karon farko, tun bayan ziyarar da kakakin majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan na kasar Sin, a ranar 2 ga watan nan na Agusta.

A jiya Lahadi, dakarun ‘yantar da al’ummar kasar Sin ko PLA reshen gabashi, ta ce ta bibiyi wadannan jiragen ruwan yaki na Amurka, kuma rundunar na cikin shirin dakile duk wata barazana.   (Saminu Alhassan)