logo

HAUSA

Masanin huldar kasa da kasa a jami'ar Abuja: Kasar Sin na sa kaimi ga sabon nau'in dunkulewar duniya

2022-08-28 16:25:56 CMG Hausa

Shugaban sashen ilimin siyasa da huldar kasa da kasa a jami'ar birnin Abuja dake tarayyar Najeriya Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, ya ce kasar Sin ta ba da gudummawa mai kyau, ga sabon nau'in tsarin dunkulewar duniya, da gudanar da harkokin mulki a duniya, kuma tana daya daga cikin masu sa kaimi ga sabon tsarin duniya. Sheriff Ghali Ibrahim, ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da manema labarai a baya-bayan nan.

Shaihun malamin ya ce an dade ana aiwatar da dunkulewar duniya, bisa jagorancin kasashen yamma, da nufin inganta tsarin siyasa, da tsarin tattalin arziki, da akidu, da al'adu irin na kasashen yamma a duk fadin duniya, domin cin gajiyar dukkanin duniya, kuma yawancin kasashen Afirka, da sauran kasashe masu tasowa, ba sa iya cin gajiyar irin wannan tsari na dunkulewar duniya.

Dangane da maganar “raba gari da kasar Sin ta fannin tattalin arziki”, da wasu cibiyoyi da 'yan siyasar yammacin duniya suka kira a yi a baya-bayan nan, Farfesa Ghali ya yi nuni da cewa, hakan na faruwa ne, kawai saboda ba za su amince da cewa, kasar Sin na samun bunkasuwa cikin sauri ba, kuma suna fargabar cewa, nasarar da Sin ta samu za ta zama abin koyi ga sauran kasashe masu tasowa, wanda hakan zai girgiza ikonsu na mallakar moriyar duniya.

Farfesa Ghali ya kara da cewa, shigar da kasar Sin cikin tsarin samar da kayayyaki na duniya, muhimmin taimako ne ga ci gaban tattalin arzikin kasashe masu tasowa irinsu Najeriya, kuma shawarar “Ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar, na ci gaba da taimakawa kasashe masu tasowa, wajen inganta ababen more rayuwa da ake bukata, domin samun ci gaba.

Kaza lika babbar kasuwar kasar Sin da ke bude kofa ga kasashen waje, tana da matukar jan hankalin kasashe masu tasowa. Ghali ya jaddada cewa, maganar “raba gari da kasar Sin ta fannin tattalin arziki”, ba za ta samu amincewa daga kasashe masu tasowa ba, saboda hakan na nufin raba gari da samun ci gaban su. A cewar masanin, “Idan babu kasar Sin, ba za a samu zarafi na ci gaba da yunkurin dunkulewar duniya ba”.   (Mai fassara: Bilkisu Xin)