logo

HAUSA

Wakilan kasashe masu tasowa daga Asiya da Afirka dake ofishin MDD na birnin Geneva sun ziyarci Xinjiang

2022-08-28 21:37:56 CMG Hausa

Bisa gayyatar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi musu, wasu jakadun kasashe masu tasowa, daga kasashen Asiya da na Afirka dake aiki a ofishin MDD na birnin Geneva, sun ziyarci jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kan ta, dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Yayin ziyarar da jami’an suka gudanar tsakanin ranakun 24 zuwa 27 ga watan Agustan nan, sun tattauna kai tsaye, da daliban da aka yaye daga cibiyoyin koyar da sana’o’i ta Xinjiang, da malaman addinin musulunci, da al’ummun kabilu daban daban dake jihar.

Bisa abubuwan da suka gani, wakilan su jinjinawa gwamnatin kasar Sin, bisa nasarorin da ta cimma a fannin dakile ayyukan ta’addanci, da kare ‘yancin al’umma na gudanar da addini, da kare martabar al’adun kananan kabilu.

Jakadun sun kuma bayyana aniyar su ta goyawa kasar Sin baya, a yunkurin ta na bayyana gaskiyar al’amari dangane da Xinjiang, da kawar da zarge zargen da wasu sassa ke yi don gane da yankin na Xinjiang.  (Saminu Alhassan)