logo

HAUSA

Bangaren masana’antun kasar Sin na ci gaba da farfadowa

2022-08-27 16:15:57 CMG Hausa

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayyana a yau Asabar cewa, harkokin bangaren masana’antun kasar Sin na kara farfadowa, duk da cewa an samu raguwar riba daga wasu daga cikin masana’antun, saboda dalilai da dama.

Cikin watanni 7 na farkon bana, manyan masana’antu, da kowannensu ke samun kudin shigar da ya kai akalla yuan miliyan 20, kwatankwacin dala miliyan 2.92, sun samu raguwar riba da kaso 1.1 idan aka kwantanta da makamancin lokacin bara, inda suka samu yuan triliyan 4.89.

Amma jimilar kudin shigar wadannan masana’antu gaba daya, ya ci gaba da habaka cikin sauri a wannan lokaci, inda ya karu da kaso 8.8, zuwa yuan triliyan 76.57.

16 daga cikin masana’antu 41 sun samu karuwar kudin shiga tsakanin watan Junairu zuwa Yuli, kana 14 daga cikinsu sun bada rahoton samun karin sama da kaso 5.

Babban jami’in kididdiga na hukumar Zhu Hong, ya ce ana samun farfadowar masana’antun kera kayayyakin aiki da masana’antu samar da motoci, yayin da ayyukan kerawa da na samar da kayyakin ke farfadowa, kana wasu manufofin da suka shafi sayen kayayyaki sun fara aiki, kamar na rage harajin sayen mota. (Fa’iza Mustapha)