logo

HAUSA

Sin na aiwatar da dukkanin matakai na kare kamfanoni da hukumomin ta

2022-08-26 10:42:03 CMG HAUSA

 

Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Shu Jueting, ta ce gwamnatin kasar na aiwatar da dukkanin matakai da suka wajaba, wajen kare hakkoki da moriyar kamfanoni da hukumomin kasar bisa doka.

Kalaman nata na zuwa ne, bayan da gwamnatin Amurka ta kara wasu kamfanonin Sin guda 7, cikin jerin kamfanonin da ta kakabawa takunkumin hana shigar da hajoji cikin kasar.

Shu Jueting wadda ta yi tsokaci game da wannan batu, yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis, ta ce Sin na matukar adawa da wannan mataki, tana kuma kira ga Amurka da ta gaggauta dakatar da irin wadannan matakai da ba su dace ba.

Sau da dama dai Amurka na bayyana dalilan tsaron kasa, da na shawo kan shigar da hajoji ba bisa ka’ida ba, a matsayin hujjar amfani da karfin gwamnati, wajen dakile ayyukan kamfanoni da sauran hukumomin kasashen waje a kasar.

Jami’ar ta kara da cewa, matakan na Amurka na matukar gurgunta harkokin musaya a fannin tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da kamfanonin kasar Sin, tare da yin watsi da ka’idojin cinikayyar kasa da kasa. Kana hakan na barazana ga tsarin samar da hajojin masana’antu da al’ummar duniya ke bukata, matakin da ba zai yiwa kasashen biyu, da ma sauran sassan duniya amfani ba.  (SAMINU ALHASSAN)