logo

HAUSA

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka ’yan ta’adda 57 yayin simame a arewa maso gabashin kasar

2022-08-26 10:34:14 CMG HAUSA

 

Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Musa Danmadami ya ce, a kalla ’yan ta’adda 57, dakarun rundunar suka hallaka, yayin wani simame da suka kaddamar a sassan arewa maso gabashin kasar.

Musa Danmadami, ya shaidawa manema labarai a birnin Abuja fadar mulkin kasar cewa, an kaddamar da hare hare ta sama da kasa ne kan maboyar mayakan kungiyoyin ISWAP da Boko Haram, dake jihohin Borno da Yobe, tsakanin ranakun 11 zuwa 25 ga watan nan na Agusta.

Danmadami ya kara da cewa, baya ga mayakan da aka hallaka, an kuma cafke mayakan kungiyoyin su 8, da masu samar musu da kayayyaki 4, tare da kubutar da wasu fararen hula 4 da suka yi garkuwa da su.

Jami’in ya kuma bayyana yadda gungun masu dauke da makamai da iyalan su mutum 1,652, ciki har da yara kanana 890, suka mika wuya ga rundunar sojojin.

Ya ce a ranar Asabar kadai, sojojin Najeriya sun yi amfani da bayanan sirri da suka samu, inda nan take suka kaddamar da hare hare ta sama, kan maboyar ’yan ta’adda dake dazukan Sambisa da Tumbuns dake jihar Borno, wanda hakan ya kai ga hallaka a kalla mayaka 25. (Saminu Alhassan)