logo

HAUSA

Xi ya karfafa gwiwar kwararrun kasashen waje da su kara ba da gudummawa wajen inganta mu'amala tsakanin Sin da sauran kasashe

2022-08-26 19:24:09 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karfafawa kwararrun masana harsunan waje a fannin wallafe-wallafe gwiwa, da su kara ba da gudummawa wajen inganta yin musaya da sadarwa tsakanin Sin da sauran kasashen duniya, da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama

Xi ya bayyana hakan ne jiya Alhamis a cikin wata wasika da ya aike wa wadannan kwararrun na kasashen waje, yayin da kamfanin wallafa littattafai ke cika shekaru 70 da kafuwa. (Ibrahim)