logo

HAUSA

An gudanar da babban taron dandalin masanan fannonin ilmi na kasa da kasa a Beijing

2022-08-26 16:40:01 CMG Hausa

A yau ne aka bude babban taron dandalin masanan fannonin ilmi na kasa da kasa a birnin Beijing, taron da ke da taken “Wayewar kai yayin da ake fuskantar manyan sauye-sauye: Sin da Duniya”, kuma shugaban sashen watsa bayanai na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Mr.Huang Kunming ya gabatar da jawabi a gun taron.

A jawabinsa, Mr.Huang Kunming ya yi nuni da cewa, a yayin da ake fuskantar kalubale na bai daya, ya zama dole a sa kaimi ga mu’amala tsakanin wayewar kai iri daban daban. Ya ce, ya kamata a kiyaye zaman daidaito da martaba juna, da kuma kara yin koyi da juna, da kuma musaya a fannin wayewar kai, don kawar da sabanin da ake fuskanta ta fannin wayewar kai.

Cibiyar nazarin kimiyyar zaman al’umma ta kasar Sin ce ta shirya taron, kuma masana sama da 100 daga kasar Sin da ma wasu kasashe 15 sun halarci taron. (Lubabatu)