logo

HAUSA

A cikin shekaru 3 Sin ta gudanar da ayyuka 713 a yankunan gwaji na ciniki cikin ‘yanci 6

2022-08-26 11:05:20 CMG HAUSA

A bana ake cika shekaru 3, tun bayan da kasar Sin ta kafa yankunan gwaji na ciniki cikin ‘yanci, a yankin tashar ruwa ta Lingang, wadda aka kafa ba da dadewa ba, dake birnin Shanghai, da ma sauran makamantan ta guda 6, dake lardunan Shandong, da Jiangsu, da Guangxi, da Hebei, da Yunnan, da Heilongjiang, tun daga watan Agusta na shekarar 2019.

A ranar 25 ga watan nan, ma’aikatar ciniki ta kasar Sin ta kira wani taron manema labarai, inda kakakinta Shu Jueting, ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu, an riga an gudanar da ayyukan gwaji 713 yadda ya kamata, a wadannan wurare 7. Ta ce:

“A cikin wadannan shekaru 3 da suka gabata, an samu ci gaba mai kyau a fannin samar da tsare-tsare a wadannan yankuna guda 7, kuma an yayata su zuwa wurare daban-daban cikin kasar, matakin da ya kara kyautata halin ciniki da ake ciki. A farkon rabin shekarar bana, yawan kudin ketare da yankin Lingang ya yi amfani da su ya kai RMB biliyan 7, wanda ya ninka sau 4.5 bisa na makamancin lokaci na bara.

A saura yankunan gwaji na ciniki cikin ‘yanci 6 kuwa, yawan cinikin shige da fice ya karu da kashi 17.1%, kuma yawan karuwar kudin ketare da suka amfani da su ya karu, da kashi 23.5% bisa na makamancin lokaci na bara, alkaluman da suka zarce na dukkanin fadin kasar da kashi 7.7%, da kuma kashi 6.1%.”

Shu Jueting ta kara da cewa, ma’aikatar za ta ci gaba da kara karfin tsai da shirin yiwa wadannan yankuna kwaskwarima, da daga matsayin bude kofar kasar ga ketare, ta yadda za a tabbatar da samun bunkasuwa mai inganci. (Amina Xu)