logo

HAUSA

Yawan shinkafan da aka noma a Sin a farkon kakar bana ya karu da kashi 0.4%

2022-08-26 19:39:08 CMG Hausa

Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta sanar a yau Juma'a cewa, yawan shinkafar da kasar Sin ta samu a farkon kakar bana, ya karu da kashi 0.4 bisa dari a bana, matakin dake nuna yadda manufofin tallafin gwamnati suka haifar da sakamako mai gamsarwa.

A cewar hukumar NBS, shinkafar da aka noma ta kai tan miliyan 28.12, karuwar tan 106,000 daga matakin shekarar 2021. (Ibrahim)