logo

HAUSA

Atisayen rundunar PLA ya dace da manufar kare ikon mulkin kai da tsaron yankunan kasa

2022-08-26 12:48:08 CMG HAUSA

 

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin Tan Kefei, ya ce jerin atisayen soji da rundunar ’yantar da jama’a ta kasar Sin PLA ta gudanar, daura da tsibirin Taiwan a kwanan baya, sun dace da manufar kare ikon mulkin kai da tsaron yankunan kasar Sin.

Tan Kefei ya yi tsokacin ne yayin da yake maida martani, ga sukar da wasu jami’an Amurka da Japan suka yi, don gane da atisayen da sojojin rundunar ta PLA suka gudanar. Ya ce "Kalaman jami’an kasashen biyu, na nuni ga yadda suke kokarin boye gaskiya, da neman shafawa kasar Sin bakin fenti, matakin da Sin din ta jima tana Allah wadai da shi.”

Jami’in ya kara da cewa, a matsayinta na wadda ta haifar da takaddamar, kamata ya yi Amurka ta dauki dukkanin alhakin abun da ya biyo baya. Ya dace Amurka ta rungumi manufar kasar Sin daya tak a duniya, ta yi kokarin gyara kurakuranta, maimakon kara ta’azzara zaman dar dar a zirin Taiwan.

Daga nan sai Tan Kefei ya yi kira ga kasar Japan, da ta waiwayi tarihinta na gallazawa wasu sassa, ta yi watsi da yada jita jita, da bata sunan kasar Sin. Maimakon haka ta mayar da hankali ga aiwatar da matakan amincewar juna tsakaninta da makwaftanta, ta kuma ingiza matakan wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin da take. (Saminu Alhassan)