logo

HAUSA

Sojojin Amurka sun kai harin sama kan kayayyakin dake kasar Sham

2022-08-25 14:05:29 CMG Hausa

Gwamnatin Amurka ta ba da sanarwa a jiya Laraba cewa, ta umarci sojojin kasar da su kaddamar da hari ta sama, kan manyan kayayyakin da dakarun fararen hula, wadanda suke yankin Ter Zor na Sham, amma suke karkashin jagorancin rundunar sojin juyin juya halin Musulunci ta Iran.

Wannan sanarwa da laftanar kanar Joe Buccino na babbar cibiyar ba da umarni ta rundunar sojin Amurka, wato USCENTCOM a takaice, ya fitar, ta ce shugaba Joseph Biden ne ya umurci kai wannan farmaki na sama.

A jiya Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanani ya bayyana cewa, harin jirgin sama da sojojin Amurka suka kaddamar a Sham, aiki ne na ta’adanci, wanda ya lahanta ikon mulkin kan kasar Sham, da zaman lafiya, da kare cikakkun yankunan kasar. (Safiyah Ma)