logo

HAUSA

MDD na neman aiwatar da shirin jin kai a arewa maso gabashin Najeriya

2022-08-25 18:54:36 CMG Hausa

Jaridar Vanguard da ake wallafawa a Najeriya, ta ruwaito kakakin babban sakataren MDD Stephen Dujarric, yana fada a birnin New York ranar Talata cewa, MDD na bukatar dala biliyan 1.1 don aiwatar da shirinta na ba da agajin gaggawa na shekara shekara, a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Sai dai a halin yanzu kashi 37 na kudaden da ake bukata don aiwatar da shirin kawai aka samu.

Dujarric ya bayyana cewa, a shekarar 2022 da muke ciki, wasu mutane miliyan 8.4 a jihohin arewa maso gabashin najeriya, za su bukaci agajin jin kai. (Ibrahim)