logo

HAUSA

Xi ya aike da wasikar taya murna ga taron hadin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka karo na biyar

2022-08-25 19:06:11 CMG Hausa

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka karo na 5.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tun bayan kafa shi shekaru 10 da suka gabata, dandalin ya samar da wata muhimmiyar kafa ga kafofin watsa labaru na Sin da Afirka, wajen inganta tattaunawa da hadin gwiwa, kana ya taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga yin musaya da yin koyi da juna, tsakanin wayewar kan Sin da Afirka, da zurfafa cikakkiyar dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi ya kuma bayyana fatan cewa, kafofin watsa labaru na kasashen Sin da Afirka, za su ci gaba da tabbatar da zumunci da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, da kokarin zama masu sa kaimi ga yin musayar al’adu da al’ummomi, masu kiyaye gaskiya da adalci, da bunkasa ci gaban duniya, ta yadda za a ba da labarin kasar Sin da kasashen Afirka a sabon zamani, da yada dabi'un bai daya na dukkan bil-Adama, da ba da gudummawar hikima da karfafa gwiwa wajen inganta gina al'umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama.(Ibrahim)