logo

HAUSA

Kasuwar Sin ta kasance mai jan hankalin masu zuba jari na kasashen waje

2022-08-25 19:40:02 CMG Hausa

A yayin taron manema labarai da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta saba gudanarwa, kakakin ma’aikatar ya bayyana Alhamis din nan cewa, bayanai daga ma’aikatar sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Yulin bana, yadda aka yi amfani da jarin waje a fadin kasar, ya karu da kashi 17.3 cikin 100 bisa makamancin shekarar 2021.

Daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, yadda ake amfani da jarin waje a duk fadin kasar, ya ci gaba da bunkasa, kuma kasuwar kasar Sin ta kasance mai jan hankalin masu zuba jari daga ketare.(Ibrahim)