logo

HAUSA

Wang Yi: Sin da Koriya ta kudu na martaba juna duk da banbance banbance tsakaninsu

2022-08-25 15:59:00 CMG Hausa

Babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce duk da banbance banbancen dake tsakanin su, kasashen Sin da Koriya ta kudu na martaba, tare da yabawa juna.

Wang Yi, ya bayyana hakan ne yayin liyafar cika shekaru 30, da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, wadda aka gudanar jiya Laraba a birnin Beijing. (Saminu Alhassan)